Saudiyya ta bude kofa ga masu yawon bude ido daga ko'ina

Hubbaren Qasr al-Farid da ke Madain Saleh na daga cikin wurare na tarihi na hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al'adu (Unesco)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hubbaren Qasr al-Farid da ke Madain Saleh na daga cikin wurare na tarihi na hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al'adu (Unesco)

A karon farko Saudiyya ta bude kofofinta ga masu sha'awar zuwa can domin yawon bude idanu daga kasashen duniya, a wani mataki na ci gaba da samun karin kudade da kokarin samun karbuwa ga sauran kasashe.

Ministan harkokin yawo bude idanu na Saudiyyar, Ahmad al-Khateeb wanda ya bayar da sanarwar ya bayyana matakin da cewa abin tarihi ne ga kasar.

Ba tun yanzu ba, tsawon shekaru kasar take ta tunanin daukar wannan mataki, wanda sai a yanzu ta yanke shawarar yin hakan.

Hakan kuma na zuwa ne a yanzu sakamakon yadda Yariman kasar, Mohammed bin Salman ke da burin ganin kasar ta rage dogaro ga mai, ta kuma fadada hanyoyin samun kudadenta.

Kafin yanzu kusan za a ce ana bai wa baki masu zuwa kasar takardar izinin shiga, wato biza, ga masu zuwa aikin ibada na Hajji da Umrah ne, sai kuma 'yan kasuwa.

To amma tun daga 'yan sa'o'in da suka gabata, da gwamnatin ta fitar da wannan sanarwa, biza na jiran masu yawon bude idanu da ke sha'awar zuwa Saudiyyar daga kasashe 49.

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman

Asalin hoton, EFA

Bayanan hoto, Yariman Mohammed bin Salman ya kudiri aniyar zamanantar da Saudiyya

Kuma dadin dadawa babu doka ko shamaki ga matan da ke son zuwa ba tare da muharraminsu ba.

Sai dai har yanzu tana jika dangane da wadanda ba Musulmi ba, game da zuwa birane masu tsarki na Makka da Madina, da har yanzu ba za a bari su je can ba.

Duk da wannan mataki na gwamnatin ta Saudiyya na bude kofofin kasar ga masu sha'awar zuwa domin yawo bude idanu, ana ganin dokokinta na Islama musamman ma kan haramcin giya a kasar, da kuma batun kisan gillar dan jaridar nan Jamal Khashoggi, a shekarar da ta wuce, wanda ake zargin hukumomin kasar da hanu a ciki, ka iya sa da dama wasu masu son zuwa, watsi da wannan dama da ta samu, da a da babu ita.

Sanin wannan ne ma kila ya sa Ministan yawon bude idanun na Saudiyyar Ahmad al-Khateeb ya ambato sassaucin da suka yi a wani bangare, musamman na tufafi, inda ya ce za a bukaci masu son zuwan su bi ka'idar abin da ya kira tufafi na kamala:

Ya ce: ''Abaya zabi ce. Ba shakka za mu fayyace wa mutane idan suka nemi biza. Za su san tsarin suturar, amma dai ta kamala ce.''

Ya kara da cewa suna da al'ada. Kuma sun yi amanna abokansu da bakinsu za su mutunta al'adar. Al-Khateeb ya ce ba ya kuma tunanin cewa harin da aka kai wa cibiyoyin mai na Saudiyya na kwanan nan zai hana mutane zuwa kasar.