'Yan majalisar Amurka sun fara shirin tsige Trump

Bayan kawar da kai da ta yi ta yi daga matsin lambar 'yan majalisar na bangaren jamiyyarta ta Democrat, a yanzu dai Nancy Pelosi ta mika wuya, kan yunkurin majalisar na kaddamar da shirin tsige Shugaba Trump.

Abin da yake a zahiri dai shi ne yunkurin da ya danganci zargin cewa Shugaba Trump ya matsa wa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ne lamba da ya yi kafar-ungulu ga damar tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden.

Ana zargin ya yi hakan ne domin yin nakasu ga shi a zaben shugaban kasar na shekara mai zuwa, kasancewar Biden din na gaba-gaba wajen damar samun takarar jam'iyyarsa ta Democrat, ta hanyar zargin rashawa a kan dan Mista Biden din Hunter.

Hunter ya kasance ma'aikaci a kamfanin makamashin iskar gas a kamfanin Ukraine tsawon shekara biyar, kuma yana daga cikin masu samun albashi mai yawa a kamfanin.

Sai dai kawo yanzu babu wata shaida ta rashawa da aka fitar.

Mista Trump ya tabbatar cewa lallai kam ya taso da batun zargin a kan Mista Biden da dan nasa, a wata tattaunawa ta waya da Shugaba Zelensky na Ukraine.

Har ma kuma ya yi barazanar daina bai wa kasar taimakon soji, ko da yake jami'an fadar shugaban Amurkar sun kafe cewa abubuwan biyu ba su da alaka, kuma babu wani tukuici ko alkawari da aka yi na saka masa da wata bukata idan ya yi abin da aka nema ya yi.

Amma dai ita Madam Pelosi tana ganin abin da shugaban ya yi ya keta haddin tsarin mulki.

A nasa bangaren Donald Trump bai bari ta kwana ba, inda nan da nan da fara shirin tsigewar, abin da ba wani shugaban Amurka da a tarihi aka yi nasarar yi wa, ya mayar da martani ta Twitter, inda ya bayyana matakin na 'yan jam'iyyar ta Democrat da shirmen makarkashiya.

Ya kuma yi alkawarin fitar da takardar ainahin tattaunawar tasu ta waya da Shugaba Zelensky da safiyar Larabar nan.

Shi ma wani dan jam'iyyar shugaban, Republic, shugaban marassa rinjaye, Kevin McCarthy ya kare shugaban yana mai cewa lokaci ya yi da za a sanya batun al'umma gaba da siyasa.

Su dai 'yan jam'iyyar Democrat suna da kyakkyawan rinjaye a majalisar wakilai, a don haka suna bukatar, ko da karamin rinjaye ne su samu amincewar aiwatar da tanadin doka na tsige shugaban kasar.

To amma inda gizo ke sakar shi ne, tsallake mataki na gaba, wato na yi wa shugaban shari'a da kuma kama shi da laifi a majalisar dattawa, da kuma uwa-uba cire shi daga ofis, wanda dukkanin wadannan abubuwa ne da suka fi wuya.

Sannan abubuwan ne da ke bukatar rinjaye da kashi biyu bisa uku, wanda kuma hakan ke nufin 'yan majalisar kusan 20, su bijire wa jam'iyyarsu, su kada kuri'ar juya baya ga shugaban.