Da waya ake tafka mafi yawan laifuka a Najeriya - Pantami
Ministan sadarwar Najeriya, Dakta Ali Isa Pantami ya alakanta karuwar miyagun laifukan sace-sacen jama'a da ake fama da su a kasar ga gibin da aka samu wajen yi wa masu amfani da layukan waya rajista.
Pantami ya ce kaso 90 na laifukan da ake tafkawa a kasar ana yin su ne ta hanyar amfani da wayar hannu musamman masu garkuwa da mutane da suke tuntubar iyalan wadanda suka shiga hannunsu ta waya domin daidaitawa a kan kudin fansar da su ke son a ba su.
Ya ce ma'aikatarsa ta sadarwa za ta tallafa wa jami'an tsaro wajen kawo karshen aikata laifukan da ake tafkawa ta wayoyin hannu ta hanyar tilasta rajistar kowane layin waya da ake amfani da shi.
A cewar Minista Pantami, satar da ake yi ta hanyar intanet ta fi satar da ake yi gaba-da-gaba.
Ya ce ya zuwa yanzu, akwai layukan waya sama da miliyan tara da ba a yi musu rajista ba, lamarin da ya ce babbar barazana ce ga kokarin gwamnati na shawo kan matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.

Asalin hoton, POLICE
Ministan ya kuma ce rashin tsaurara mataki daga kamfanonin wayoyin kan rajistar layi na kara bai wa masu muguwar aniya da damar yin ta'asa, wanda a cewarsa, akwai layukan waya kimanin miliyan 9.2 da ba su da rajista.
Ya kara da cewa akwai wasu layukan waya miliyan 6.7 da aka rufe saboda rashin sanin ainihin masu amfani da su.
Ministan ya bayyana cewa nan gaba akwai layukan waya miliyan 2.4 da za su tantance a yunkurin da suke yi na hana aikata laifuka ta hanyar amfani da layukan waya.
Sai dai kuma wannan yunkuri na tantance layukan waya ta hanyar yi musu rajista na iya jefa kamfanonin waya cikin mawuyacin hali ta yadda a kididiiga za su rika asarar naira biliyan 14 a kowane wata.











