Mai kisan mata a Fatakwal ya ce '15 ya kashe a otal'

Asalin hoton, NIGERIA POLICE
Hukumomin 'yan sanda a Najeriya sun ce mutumin da ake zargi da kisan 'yan mata a gidajen otal-otal a birnin Patakwal ya tabbatar shi ne ya kashe wasu mata 15 sabanin mutum bakwai da tun farko ya ce ya halaka, a wani taron manema labarai.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar Rivers, Mustapha Dandaura ya ce wanda ake zargin ya ambata cewa shi ne ya halaka 'yan matan sakamakon wani bincike da 'yan sandan suka zurfafa a otal-otal din da ya kashe matan.
Kwamishinan ya kara da cewa: ''A taron manema labaran, wanda ake zargin ya ce shi kawai mutum biyar ya halaka sai dai bayan taron.
"Mun sake yi masa tambayoyi inda ya kai mu dakunan da ya yi aika-aikar, daga nan ne kuma ya ce ai mata bakwai ya kashe."
Kwamishinan ya kara da cewa "mutumin ya ce ya kashe daya a Legas da kuma wasu dai-dai a Owerri da Sapele da Aba da Benin har ma da Badun, abin da a jimulla ya halaka mata 15 kenan.
"Guda tara a Fatakwal, da kuma wasu shida daban a wasu yankunan da ke wajen Fatakwal. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka gabatar da shi ga manema labarai,'' in ji kwamishinan 'yan sandan.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamishinan ya kuma ce, bayan da suka gabatar da mutumin gaban 'yan jarida, ranar Juma'ar da ta gabata, rundunonin 'yan sanda na jihohin Najeriya sun tuntube su kan cewa wanda aka kaman, su ma suna zargin shi ne ke da hannu a kashe wasu matan a jihohinsu.
Kwamishina Dandaura ya kuma ce: ''Tuntuba ta karshe da aka yi mana ita ce jiya Litinin.
Wasu mata 'yan sanda a sashen binciken manyan laifuka sun zo daga Aba tafe da hoton wata mata da ake zargin mutumin ya kashe ta hanyar daure mata hannayenta da kafafuwa, irin salon kisan da ake zargi ya yi wa sauran 'yan matan.

Asalin hoton, Others
Kwamishinan ya ce, na'urar daukar hoto ta tsaro ta nuna mutumin sanye da irin kayan da ke jikinsa, wanda saboda haka ya ba wa jami'an 'yan sandan mata izinin su yi masa tambayoyi.
Ya ce, suna ganin mutumin, suka ce shi ne ya yi aika-aikar kuma shi ma wanda ake zargin bai musa ba.
Dandaura ya kuma bukaci tawagar 'yan sanda ta musamman da aka kafa domin sa ido da tabbatar da aiwatar da sabbin ka'idojin da aka gindaya wa masu otal-otal, da su gudanar da aikinsu da kuma bibiyar gidajen otal-otal din da ke kananan hukumomi.
Ya kuma ba da umarnin garkame duk wani otal da aka samu da karya dokokin da aka shimfida domin hakan ya zama izina, ga masu niyyar tafka mugayen ayyuka kamar yadda aka yi game da sace-sacen jama'a.
Ya kuma ce da a ce otal-otal din sun dauki shawarar sanya na'urar daukar hoto ta tsaro ta da kuma daukar bayanan abokanan huldarsu, da sun iya gano wannan mai kashe-kashen matan tun da wuri, sannan kuma adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar hakan da ba zai kai yadda ya kai ba yanzu.
Ana sa ran nan da wasu 'yan kwanaki, 'yan sanda za su gurfanar da wanda ake zargin a kotu.











