Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ji karar fashewa da harbe-harbe a Jami'ar Maiduguri
Wasu rahotanni daga Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya sun sheda wa BBC cewa an ji fashewar bama-bamai da harbe-harben bindiga a kusa da jami'ar da misalin karfe tara da rabi na dare ranar Lahadi.
Wasu dalibai da ke ta gudun neman tsira a lokacin sun bayyana yadda suka ji karar fashewar da harbe-harben, lamarin da ya firgita su, suka rika gudu.
Duk da cewa dai babu wani cikakken bayani game da wadanda suka kai harin, amma dalibai sun yi amanna cewa mayaka ne na kungiyar Boko Haram, da ke ikirarin jihadi.
Haka kuma babu wani cikakken bayani game da wadanda harin ya rutsa da su.
Rahotanni sun ce an tsaurara tsaro a jami'ar, kuma gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum da tawagar sojoji sun je harabar jami'ar inda bayanai suka ce komai ya layafa.
Sai dai kuma wasu rahotanni na cewa ba cikin jami'ar aka kai harin ba, saboda kawai kusanci da inda lamarin ya auku ne dalibai suka ji kamar jami'ar aka kai wa harin.