Carrie Lam ta janye kudurin doka mai bakin jini

Shugabar birnin Hong Kong, Carrie Lam ta sanar da janye kudurin dokar nan mai matukar bakin jini da shi ne dalilin tashin hankali na siyasa da ya mamaye birnin a watannin da suka gabata.

A wani mataki da ake ganin babban koma baya ne ga shugabar birnin da gwamnatin China, janye kudurin dokar na cikin matakan da ake ganin za su kwantar da hankulan mutanen birnin.

Wata uku kenan masu zanga-zanga a HK ke kira ga gwamnatin birnin ta janye kudurin doka da ke neman aikawa da wadanda ake tuhuma da aikata laifi zuwa China domin a yi musu shari'a.

Dubun-dubatar 'yan yankin kuma suna adawa da kudurin kuma sun nuna haka ta fita bisa titunan birnin

A wasu lokuta ma wasu masu adawar - wadanda kuma ke da tsattsauran ra'ayi sun rika daukan matakai kamar jefa bama-bamai irin na fetur a karawarsu da jami'an 'yan sanda.

Amma duk wannan ya kau - domin jagorar birnin Carrie Lam ta janye kudurin dokar a hukumance, kuma ba za a gabatar da kudurin ba a gaban majalisar da ke yi wa birnin dokoki a zamansa na watan Oktoba.

Amma duka da wannan labari mai dadin ji, yawancin masu zanga-zanga a HK sun ce ba za su daina yin gangami ba har sai an kafa wata hukuma mai zaman kan ta da za ta duba abin da suka kira alakar da 'yan sandan HK suke da ita masu aikata manyan laifuka.

Mutanen birnin kuma na son a basu damar zaban shugaban birni tare da 'yan majalisar birnin kai tsaye - matakin da ya sha bamban da na yanzu - wanda suke ganin an shirya ne domin China ta rika nuna ikonta kan birnin.