An kama matar da ta kulle yaro a kejin kare

Asalin hoton, @opetodolapo
'Yan sanda a birnin Legas na Najeriya sun kama wata mata da aka dauki hotonta tana cin zarafin wani yaro sannan ta kulle shi a wani keji na karnuka.
Babu tabbas kan lokacin da aka dauki bidiyon amma an rinka yada shi a shafukan Twitter a farkon watan nan.
An ga matar a bidiyon, tana dukan yaron da bel.
Daga nan sai ta saka shi a wani keji ta rufe sannan ta kama gabanta.
Akwai wasu karnuka biyu a cikin wani keji kusa da wanda ta saka yaran.
Bidiyon ya tayar da hankulan mutane a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi alkawarin bayar da lada ga duk wanda ya taimaka aka gano inda matar take.
A ranar Alhamis, mai magana da yawun 'yan sanda, Dolapo Badmos, ta wallafa a shafin Twitter cewa an kama matar.
Ta ce "Matar na hannun jami'an tsaro kuma za a gurfanar da ita a kotu... An kubutar da yaron, wanda maraya ne, kuma ana kula da shi a wani wurin mallakin gwamnatin Legas."
Sakon da ta wallafa na dauke da shafin wani bidiyo wanda 'yan sanda suka nada da ke nuna kejinan da aka kulle yaron:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











