'Yan Katsina da Zamfara sun kwarara Nijar

'Yan gudun hijira
Bayanan hoto, Mata da kananan yara da tsofaffi sun fi shan wuya a lokutan tashin hankali irin wannan

A Jamhuriyar Nijar alkaluman da hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna an samu karin 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallansu a cikin kasar.

Wannan na kunshe cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, inda ya nuna tashe-tashen hankulan da masu ikirarin jihadi irin na kungiyar Boko Haram na daga cikin matsalar da ta daidaita jama'a suka bar muhallansu.

Yawancin 'yan gudun hijirar dai sun fito ne daga kasashe makofta, inda alkalumman suka nuna an samu kwararar 'yan gudun hijira daga kasar Mali da suka kai 56,000 kamar yadda ministan ma'aikatar agaji na jamhuriyar Nijar Malam Lawan Magaji ya shaidawa BBC.

Sai kuma 'yan gudun hijira da suka tserewa tada kayar bayan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, wadanda ke zaune a jihar Diffa tun shekarar 2015 da suka kai 10,8000.

A baya-bayan nan tashe-tashen hankulan da suka addabi jihohin Zamfara da Katsina na barayin shanu da garkuwa sun janyo 'yan gudun hijira sama da 20,000 sun sake kwarara kasar Madarumfa da gidan Rumji a jamhuriyar Nijar.

Tabarbarewar tsaro a iyakar Nijar da Burkina Faso ta bangaren arewaci a yankin Udala, da Dori ta taka muhimmiyar rawa wajen sake kwararar 'yan gudun hijirar ciki har da 'yan kasar mazauna iyakunan da lamarin ya fi kamari.