Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin jihar Zamfara ya fara yin awon gaba da masu sarauta
Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Muhammad Mutawalle ya dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Chika Ibrahim da Hakimin Kanoma, Alhaji Ahmad Lawal bisa zargin hannu a taimaka wa barayi masu sata da kisan jama'a.
Wata sanarwa da darektan watsa labaran gwamnatin ta jihar Zamfara, Alhaji Yusuf Idris, ya fitar, ta ce an dakatar da masu rike da sarautun guda biyu bayan samun korafe-korafe daga talakawansu kan taimaka wa barayi da kuma sauran ayyukan bata-gari.
Sanarwar ta ce an dakatar da Sarkin na Maru da hakimin na Kanoma har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
An kuma umarci masu sarautun da su mika dukkanin kayan gwamnati da ke hannunsu kamar mota ga manyan masu sarauta a fadarsu.
'Yan uwan Sarki sun musanta zargi
Alhaji Bala A Ibrahim sarkin Sudan na Maru, dan uwa ne ga Sarkin na Maru, Alhaji Abubakar Chika Ibrahim wanda na daya daga masu sarautar da aka dakatar.
Alahji Bala ya ce, sam-sam zargin ba shi da tushe ballatana makama, inda ya alakanta abun da aikin masu hassada ga sarkin.
Ya kara da cewa Sarkin na Maru ya sha samun barazana daga barayin da masu kisan jama'a ta waya, inda kuma yake yawan aika takardun neman dauki daga jami'an tsaro.
Dan uwan sarkin ya ce, "a je a duba kundin jami'an tsaro za a takardun da sarki ya rubuta na neman kai masa dauki."
Ya kara da cewa "ta ya ya za a zargi Sarki bayan yana daya daga cikin sarakan da suka sadaukar da kansu wajen yakar bata-gari?"
An dade dai ana zargin masu sarauta da hannu a rikicin da ke faruwa a jihar ta Zamfara.