'Najeriya na da 'yan gudun hijira miliyan 1.2'

Wani rahoto da aka fitar kan 'yan gudun hijira ya nuna cewa akwai mutum miliyan 41 da ke gudun hijira a fadin duniya.

Rahoton ya bayyana cewa 'yan gudun hijiran miliyan daya da dubu 200 cikin miliyan 41 daga Najeriya suka fito.

Rahoton ya bayyana cewa rikice-rikice da ake yi a nahiyar Afirka ya bayar da gudummawa wajen karuwar yawan mutanen.

Hakazalika, rikice-rikice da kuma bala'o'i daban-daban da aka yi fama da su a fadin duniya sun tursasawa mutum miliyan 28 su bar gidajensu zuwa wasu sassan duniya.

Wannan yawan ya karu da kusan miliyan daya tun a karshen 2017.

'Yan gudun hijirar da suka fi yawa sun fito daga kasar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo da kuma Syria wadanda kasashe ne da suka dade suna fama da rikice-rikice.

Ethiopia ita ma na daga cikin kasashen da suke kan gaba a jerin gwanon kasashen da 'yan kasar suke gudun hijira inda kasar ke da masu gudun hijira miliyan uku a 2017.

A fadin duniya, iftila'oi kamar su ambaliyar ruwa da wutar daji da fari sun bayar da gudummawa wajen raba mutane da muhallansu daga kasashe kamar China da Indiya da Philippines.

Sakatare Janar na wata kungiya ta masu gudun hijira na kasar Norway wato Jan Egeland ya bayyana cewa ''wannan rahoton kamar wani kira ne ga shugabannin duniya, mutane da dama sun bar muhallansu sakamakon nuna halin ko in kula daga gwamnatoci da kuma karancin diflomasiya daga kasashe.''

Ya kuma bayyana cewa ''duk da cewa masu gudun hijrar na bakin iyakoki, amma kasashen duniya basu cika nuna damuwa kansu ba. Duk 'yan gudun hijira na da hakkin kasashen duniya su kare su.''