Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe mutane da dama a Zamfara
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar Dakta Suleiman Shu'aibu Shinkafi da wakilinmu Mustapha Musa Kaita:
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 30 ne suka rasa ransu a wani hari da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai a garin kwari da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Dakta Suleiman Shu'aibu Shinkafi wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a ranar kasuwar Shinkafi, a daidai lokacin da jami'an sa-kai suke kokarin raka jama'a domin cin kasuwa.
Ya shaida cewa a ranar kasuwar, barayin sun bude wa jami'an sa-kai da kuma 'yan kasuwar wuta inda suka kashe su gaba daya.
Dakta Shinkafi ya koka bisa rashin tsaron da suke fama da shi a wannan yankin na Shinkafi, inda ya bayyana cewa akwai karancin sojoji da 'yan sanda.
Kuma jami'an sa-kai ne "suke taimaka wa jama'a a wannan yankin."
BBC ta tuntubi kakakin 'yan sanda na jihar, inda ya tabbatar da faruwar lamarin amma babu wani cikakken bayani a kan adadin mutanen da suka mutu ko kuma jikkata.
Sai dai kakakin 'yan sandan ya ce suna gudanar da bincike kuma za su yi karin bayani idan sun kammala.
An dade ana fama da rashin tsaro a yankin Zamfara, inda har a kwanankin baya wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kashe akalla mutum 15 a kauyen Magamin Diddi cikin yankin karamar Hukumar Muradun a jihar Zamfara.
Haka ma wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun kashe yayar Sanata Kabiru Marafa, a wani hari da suka kai a kwanakin baya a Tudun Wadan Mai Jatau da kuma Ruwan Baure cikin jihar Zamfara.