Kukan yaran Yemen ya kai ga Ubangiji - Fafaroma Francis

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fafaroma Francis tare da Yariman Abu Dhabi

Fafaroma Francis ya roki bangarorin da ke yaki da juna a Yemen da su tuna da halin da miliyoyin 'yan kasar ke ciki na yunwa da rashi.

Fafaroman na magana ne daf da ya tashi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin kai wata ziyara irinta ta farko zuwa yankin da wani fafaroma ya taba kai wa.

Fafaroman ya yi wannan kiran ne a yayin da yake yin jawabi ga mabiya darikar katolika a Fadar Vatikan.

Ya ce kukan yaran kasar Yemen ya kai ga ubangiji, kuma ya roki bangarorin masu yaki da juna da su tabbatar sun kyale tallafin abinciu da magani ya isa wurin miliyoyin fafaren hula da yakin ya rutsa da su.

Ana dai sukar wannan ziyarar ta Fafaroman zuwa Abu Dhabi ganin cewa dakarun Hadaddiyar Daular Larabawa na marawa bangaren gwamnatin Yemen a yakin da ta ke yi da 'yan tawayen Hothi.

Amma ya kare kansa, inda ya ce wannan ziyarar zuwa wurin da ya kira mahaifar Musulunci dama ce ta zurfafa dangantaka tsakanin manyan addinan duniya biyu - wato Musulunci da Kiristanci.