Mata masu jinin Haila na mutuwa a Nepal

Wata matashiya 'yar shekara 21 daya ta rasu saboda tsananin zafin da hayaki da ke cikin Bukkar da akan kebewa mata a lokacin da suke jinin Haila, sakamakon hura wuta da ta yi dan ta ji dumi.

Lamarin ya faru ne a gundumar Nepal Doti da ke kasar India, hakan kuma ya zo makwanni biyu bayan wata Uwa da 'ya'yanta biyu suka mutu kan lamarin wannan.

Hukumomin Nepal dai sun haramta dadaddiyar al'adar nan ta kebewa mata muhalli a lokacin da suke jinin al'ada saboda dalilai da suka shafi addinan gargajya da canfi.

Wata mace mai suna Niha Sharma ta shaidawa BBC cewa a duk lokacin da ta ke al'ada ba ta da izinin taba ko da cokalin cin abinci ne bare kuma dafa abincin kan shi.

Sannan maigidanta baya kula ta, ko shiga sabgarta da sauran jama'ar gida, a cewarsu ba ta da tsarki.

Al'adar da ake kira Chhaupadi dai ba matan da suke jinin al'ada kadai ta shafa ba, har da matan da ba su dade da haihuwa ba wadanda ke cikin jinin biki.

An cafa cewa zama wuri daya da su, ko mu'amala da su wani mugun abu zai iya samunsu. Haka kuma ana tilasta musu kwana har a inda dabbobi kamar karnuka ke kwana da sauran wurare maras tsafta.

Tun a shekara ta 2005 aka rattaba hannu kan dokar amma har yanzu ana amfani da ita musamman a yankunan karkara.