Isra'ila ta kai wa sojojin Iran hari a cikin Syria

Isra'ila ta bayyana cewa ta kai wa dakarun Iran dake kusa da babban birnin Syria, Damascus, hari.
Isra'ila ta bayyana cewa a cikin dare ne ta kaiwa manyan dakarun Iran hari, da kuma dakarun sojojin sama na Syria.
Amma dakarun kasar sojin Syria sun bayyana cewa sun harbo rokokin na Isra'ila, amma wata kungiyar sa ido ta bayyana cewa an kashe dakarun Syria 11.
Dakarun Isra'ila sun bayyana cewa sun harba nasu rokokin ne bayan da dakarun Iran suka harba wasu bama-bamai zuwa tsibirin Golan Heights.

Kasar Iran, wadda ke adawa da Isra'ila, na goyon bayan shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad, inda ta tura dubban sojojinta domin su tallafa masa a yayin da kasarsa ke ci gaba da fuskantar yakin basasa.







