Zaben 2019: Abin da ke sa 'yan siyasa yin alkawarin bogi

Matasa a Najeriya na zargin 'yan siyasa da kin cika alkawurra

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin da zabe ke matsowa, 'yan siyasa kan rinka yawon kamfe domin ganawa da al'umma da kuma shaida masu ayyukan da suke sa ran aiwatarwa idan sun samu nasara.

Wani matashi a Najeriya, Bello Bala Shagari ya ce da yawa irin wadannan alkawurra da 'yan siyasar kan yi kan tafi ne ba tare da an aiwatar da su ba.

A cewarsa "Yawanci 'yan siyasa ba su cika kashi hamsin zuwa sittin na alkawurran da suke yi."

Ya kara da cewa hakan na faruwa ne saboda 'yan siyasar na yin alkawurran ne ba tare da yakinin cewa za su iya cika su ba.

"'Yan siyasa sukan yi alkawurra, har da wadanda ba su san yadda za su cika su ba."

Sau da yawa sukan yi alkawurran, amma a lokacin da suka ci zabe sai su gane cewa ba za su iya cikawa ba-In ji Shagari

"'Yan siyasar kan yi irin wadannan bayanai ne saboda suna neman kuri'a ko kuma saboda suna tunanin ayyukan na da sauki."

Wata matashiya a Najeriya Hafsatu Umaru Shinkafi ta ce 'yan siyasa kan yi wa mata dadin baki a lokacin yakin neman zabe.

Sai dai ta ce matsalar da ake fuskanta ita ce akan manta da matan da alkawurran da aka masu bayan an ci zabe.