Majalisar Amurka na nuna mana kiyayya — Saudiyya

Tsawon shekara hudu yanzu da Yemen ke fama da yaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsawon shekara hudu yanzu da Yemen ke fama da yaki

Saudiya ta yi watsi da kudirin majalisar dattawan Amurka na kawo karshen taimakon sojin da Amurka ke bai wa dakarun kawance da kasar ke jagoranta a yakin Yemen da kuma dora alhakin kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a kan yarimar Muhammad bin Salman.

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyar ta bayyana matakin da wani katslanda da kuma zarge-zarge marasa gaskiya ko sahihanci.

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne 'yan majalisar suka amince da kudirin a wata kuri'a da suka kada, wadda babu mamaki ta zama doka.

A watan da ya gabata Amurka ta dakatar da jiragenta na yaki da ke taimakwa Saudiya, idan kuma wannan kudiri ya zama doka, to zai haramta dawo da wannan taimako baki daya.

Wata sanarwa da kafar yada labaran Saudiyar ta wallafa, ta ce kasar ta yi alla-wadai da wannan matsayi.

Ta ce an gina wadanan zarge-zarge ne a kan karya tsagwaranta da kuma tir da duk wata kasa da ke shiga harkokin cikin gidanta.

Har yanzu dai a fili Amurka ba ta mayar da martani a kan kalaman Saudiyar ba.

Sai dai Saudiyar ta aike da sakon gargadin ga shugaba Donald Trump a kan abin da ta kira kiyayya da 'yan majalisar dokokin kasar ke nuna wa a kan tsare-tsare kasarta.

Kudirin da ba a tabbatar da shi a matsayin doka, ya bukaci mista Trump da ya janye duk wani taimakon soji ko na makamai da kasar ke bayarwa a yakin Yemen, sai dai idan batu ne daya shafi murkushe kungiyoyin jihadi.

Sanatocin sun kuma amince da kudurin da ya doro alhakin mutuwar Jamal Khashoggi a kan Yarima Muhammadd Bin Salaman, da kuma jadada cewa dole masarautar kasar ta fito fili ta yi bayyani a kan kisan.

Wannan dai shi ne karo na farko da majalisar Amurka suka amince da wani kudiri na neman janye taimakon soji da kasar ke bayarwa a yaki.