Mujallar Time: Khashoggi da wasu 'yan jaridu ne 'Gwarzayen Shekarar 2018'

Asalin hoton, Time
Mujallar Time ta zabi 'yan jaridar da aka kashe ko ake tsare da su a matsayin gwarzayen shekara ta 2018.
Mujallar ta wallafa shafukanta na farko guda hudu inda aka sa 'yan jaridun da hukumomi suka sa a gaba saboda aikin da suke yi a bana.
Sun hada da Jamal Khashoggi wanda aka kashe a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya
Wasu 'yan jarida masu aiki a jaridar nan ta Amurka mai suna Capital Gazette inda aka kashe wasu abokan aikinsu biyar suma sun sami shiga jerin gwarzayen shekara tare da Maria Ressa ta kasar Filifins da kuma matan 'yan jaridan Myanmar Wa Lone da Kyaw Soe Oo.

Asalin hoton, Time

Mujallar Time ta ce ta zabe su ne saboda "sadaukar da rayukansu da suka yi domin fayyace gaskiya, da kuma kokarin da suke yi na bayyana zahirin abubuwan da ke faruwa".
Su waye 'yan jaridar?
Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi sanannan dan jarida ne dan kasar Saudiyya wanda kuma ke sukar hukumomin kasarsa. Ya bace bayan da ya ziyarci ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya a watan Oktoba.

Asalin hoton, EPA
Mista Khashoggi na gudun hijira a Amurka ne, inda yake aiki da jaridar Washington Post. Ya tafi birnin Santanbul ne domin karban takardu dangane da auren wata budurwarsa 'yar Turkiyya da yake son yi.
Ma'aikatan jaridar Capital Gazette
A ranar 28 ga watan Yuli wani dan bindiga ya shiga ofishin jaridar Capital Gazette a birnin Annapolis da ke jihar Maryland inda ya kashe ma'aikatan jaridar su biyar.,
Daga baya bincike ya nuna cewa dan bindigar na hakon jaridar na dadadden lokaci bayan da ya kasa sa wata kotu ta biya shi diyya kan wata kara da ya kai jaridar a shekarar 2012.
Amma wannan tashin hankalin bai hana ma'aikatan ci gaba da aiki daga filin da ake ajiye motoci ba, wanda ya sanya suka iya wallafa jaridar da ta fita kashegari.
Ban da wallafa sakonnin mutuwar abokan aikinsu, sun bar shafin da ake wallafa sharhi fayau babu rubutu saboda ba su da abin cewa, kamar yadda suka wallafa.

Asalin hoton, AFP
Maria Ressa da Rappler
Tsohuwar 'yar jaridar tashar CNN Maria Ressa ta samar da shafin labarai na intanet mai suna Rappler a kasar Filipins a shekara 2012, kuma ba a dade ba ta yi fice saboda ingantattun labaran da take samarwa.
Kafar labaran ta rika sukar shugaban kasar Rodrigo Duterte har ta kai tana binciken sahihancin kalaman da yake yi a bainar jama'a game da yaki da miyagun kwayoyi.

Asalin hoton, EPA
Watanni bayan da aka zabe shi a 2016, Rappler ta wallafa wani cikakken rahoto kan yadda aka rika amfani da na'ura mai kwakwalwa da shafukan sada zumunta na Facebook na bogi wajen watsa sakonnin da ke zuzuta yawan goyon bayan da shugaban ke da shi.
Daga nan Mista Duterte ya fara sukan shafin watsa labaran, inda ya kira shi karkatacce har ya hana mai aika rahotanni daga jaridar aiki a fadar shugaban kasa.
A watan Janairun bana hukumomin kasar suka kwace lasisin da aka ba Rappler, matakin da ya janyo kace-nace daga al'ummar kasar kan 'yancin aikin jarida.
A watan nan na Nuwamba kuma aka tuhumi Maria Ressa da jaridar ta da kin biyan haraji - matakin da ta musanta.
Wa Lone da Kyaw Soe Oo
'Yan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters Wa Lone da Kyaw Soe Oo 'yan kasar Myanmar ne, kuma an daure su a kurkuku na tsawon shekara bakwai a watan satumbar da ya gabata saboda wai sun bayyana labaran sirrin gwamnatin kasar.
Wannan ya biyo bayan wani aiki da suka yi ne a watan satumbar 2017 na binciken kisan da sojin Myanmar su ka yi na wasu 'yan kabilar Rohingya su 10 a kauyen Inn Dinn da ke yankin Rakhine.

Asalin hoton, AFP
Daga nan aka kama 'yan jaridar su biyu a Disambar 2017 yayin da suke dauke da wasu takardun gwamnati da wasu 'yan sanda biyu suka basu.
Sun musanta aikata wani laifi, inda suke cewa 'yan sandan kasar ne suka yi masu cinne.










