Atiku Abubakar ya kaurace wa taron zaman lafiya

Dan takarar babbar jam'iyar hamayya a Nijeriya wato PDP, Atiku Abubakar, ya kaurace wa taron sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin manyan zabukan shekarar 2019 a kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari da wasu 'yantakarar da dama sun halarci taron kuma sun sa hannu a 'yarjejeniyar.

An sa hannun ne a kan idon malaman addinai da sarakunan gargajiya da kuma jakadu na kasashen Turai.

Tsohon shugaban Najeriya Janar mai ritaya Abdussalam Abubakar wanda shi ne shugaban kwamitin kulla wannan yarjejeniyar ya bayyana wa wakilin BBC Is'haq Khalid cewa bai san dalilan da suka hana Atiku Abubakar halartar taron ba.

Ya ce "Kafin mu zo wannan taron sai da muka zauna tare da dukkan jam'iyyun siyasar kasar nan. Bayan da muka sami matsaya ne aka sa ranr kulla wannan yarjejeniyar."

Ya kuma ce baya jin rashin zuwan dan takarar babbar jam'iyyar adaa ta PDP zai shafin ingancin yarjejeniyar da aka kulla.

"Mutum daya domin bai zo ba, yaya zai rusa dukkan abin da aka yi? Nayi mamakin da wasu basu zo ba, domin sai da muka zauna aka cimma matsaya."

A nasa bangaren shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an sha samun matsalolin zabe a baya saboda halayyar da wasu 'yan siyasa da magoya bayansu ke nunawa.

Ya kara da cewa "Akwai alamu masu karfafa gwuiwa da ke nuna cewa a wannan karon, 'yan siyasa na son taka rawar da ta dace da su domin kawo cigaba da zaman lafiya."

Martanin jam'iyyar PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa a shirye ta ke ta yi duk mai yiwuwa domin a gudanar da zabukan shekarar 2019 cikin zaman lafiya da lumana.

Jam'iyyar ta bayyana takaicinta na raashin halartar taron, tana cewa an sami matsalar samun cikakken bayani ne tsakanin jam'iyyar da kwamitin da ya shirya kulla yarjejeniyar a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar.

Jam'iyyun siyasa da dama ne suka halarci wannan taron na ranar Talata a Abuja domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan siyasar kasar.

Jam'iyyar ta ce tana gudanar da binciken cikin gida domin ta gano abin da ta kira "yadda wannan abin takaicin ya auku."

Ta kara da cewa "Jam'iyyarmu za ta ziyarci ofishin kwamitin zaman lafiya na kasa domin ganin abin da yarjejeniyar ta kunsa, sannan ta dauki dukkan matakin da ya kamata ta dauka domin tabbatar da zaman lafiya alokacin zabukan shekarar 2019."