An sako tagwayen da aka sace a Zamfara

Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun sako 'yan matan nan tagwaye da suka sace a watan jiya.

Dangin tagwayen da kuma wani babban jami'i a Karamar Hukumar Zurmi daga inda aka dauke su, sun tabbatar wa BBC da sakin nasu.

Kuma sun ce suna cikin koshin lafiya.

Sai dai kuma sun ce ba a sako yayarsu ba - wacce aka kama su tare a wani gida da ke garin Dauran a watan jiya a yayin da suka je rabon katin bikin aurensu.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000

Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya.

Karanta karin wasu labarai masu alaka: