Guguwar Florence na gab da isa Carolina

Arewacin Carolina
Bayanan hoto, Guguwa da ruwa mai karfin gaske sun fara hana motoci wucewa

Hukumar kare bala'in guguwa a Amirka ta sanar da cewa a yanzu guguwar Florence na nisan kilomita 95 daga gabar tekun arewacin Carolina, kuma ta na tafe da wata kakkarfar iska mai gudun kilomita 150 cikin sa'a guda.

Masu hasashen yanayi sun ce a yau juma'a guguwar za ta arewacin Carolina kafin daga bisani ta nufi kudu maso gabashi.

Tuni aka fara batun kwashe mazauna yankunan da abin zai shafa.

Daraktan hukumar agajin gaggawa ta kudancin Crolina Mike Sprayberry, ya ce sun koyi darasi daga guguwar da ta faru a shekarar 2016.

A lokacin da guguwar Matthew ta afku, a wancan lokacin an yi amfani ne da taswirar wuraren da ake zaton za su fuskanci ambaliyar ruwa.

Sai akai kokarin sanar da hukumomin yankunan dan su san yadda za su tsara kwashe mutane, dan ba a bukatar kwashe mutanen akai su wani wurin da watakil zai fuskanci ambaliya ba a sa ni ba.

Cibiyar nazari kan bala'u ta nuna fargabar za a fuskanci ambaliyar ruwa fiye da hasashen da aka yi tun da fari, kuma dubban mazaunan yankin ne suka kauracewa gidajen.