Da gaske an yi wa Kwankwasiyya tawaye a Kano?

Wasu da suka yi ikirarin magoya bayan Kwankwasiyya ne sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a daidai lokacin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar takararsa ta neman shugabancin kasar a Abuja.

Daruruwan matuka babura masu kafa uku ne da aka fi sani Adaidaita Sahu a Kano da ke ikirarin cewa mabiya akidarsa ta kwankwaisiyya ne su kai wannan sauyi zuwa bangaren Gandujiyya mai mulki.

Jami`an gwamnatin jihar Kano ne suka karbe su, a wajen wani biki na musamman da aka gudanar a Kano ranar Laraba.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu kafofin watsa labaran jihar suka ruwaito cewa wasu masu baburan Adaidaita Sahu din suka yi ikirarin sauya shekar, sun yi korafin cewa ba a biya su kudin da aka yi musu alkawari ba.

Wasunsu sun shaida wa wani gidan rediyo mai zaman kansa cewa, an tare su ne kawai a hanya aka ce "su je taron za a biya su, amma kuma sun nemi wanda zai biya su sama ko kasa sun rasa."

Ana dai zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce ta shirya bikin domin dauke hankalin jama`a daga taron da tsohon gwamnan ya shirya a Abuja, sai dai gwamnatin ta musanta hakan.

Amma kwamishinan watsa labaran jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya ce sam ba haka lamarin yake ba.

Ya ce mutanen ne suka shirya sauya shekar don radin kansu, amma ba wai gwamnati ce ta dauki nauyin su ba.

Shugaban jam`iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas shi ne ya jagoranci bikin karbar su, wadanda suka yi ikirarin cewa sun kai akalla mutum dubu biyar.

Shugaban `yan Adaidaita Sahun, Malam Usama Haruna Dala ya ce rashin kyautatawa ne ya tilasta musu kaurace wa gidan kwankwasiyya.

Wannan sauya sheka da `yan Adaidaita Sahu suka yi dai ba karamin kamu ba ne a wajen jiga-jigan gwamnatin APC a jihar Kano, kamar yadda Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara na jihar Kano ya bayyana, inda ya ce sun gama tatike kwankwasiyya saura jagoranta:

An dade da raba-gari tsakanin gwamna Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, amma adawar ta kara tsami ne bayan ficewar Kwankwason daga APC zuwa jam`iyyar PDP.

Kuma mabiya Gandujiyya da dama na kallon wannan neman takarar shugabancin kasar da Kwankwason ke yi a matsayin cin fuska ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin Najeriyar bai haramta masa yin haka ba.