Ebola ta zama alakakai a Congo

Asalin hoton, Getty Images
Hukomomin lafiya a jamhuriyyar demokuradiyyar Congo sun fara shirin tunkarar yaki da cutar Ebola wacce ta sake bulla a kasar kuma yanzu ke ci gaba da barazana ga rayukan jama'a.
Mutune sama da 43 aka ruwaito sun kamu da cutar yayin da alkalumman farko na ma'aikatar lafiya a kasar suka ce mutane 30 sun mutu.
Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce za ta tura tawagar likitoci zuwa yankin arewa maso gabashi kusa da iyaka da Uganda inda cutar ta sake bulla.
Jami'an lafiya sun fara sanya allurar riga-kafin cutar a cikin firji domin sanyaya maganin.
Ma'aikatar lafiyar ta ce a ranar laraba take fatan jami'anta za su fara aikin yaki da cutar.
An dai yi nasarar gwajin rigakafin maganin wanda wani kamfanin hada magunguna na Macrk ya samar.
Kuma gwamnatin kasar ta ce tana da sama da 3000 na rigakafin maganin da ta ajiye a Kinshasa, wanda ke bukatar a jiye shi wuri mai sanyi da kankaara
Babbar matsalar da jami'an lafiya ke kokawa shi ne makwanni kalilan allurar ke yi a ajiye ba tare da an yi amfani da ita ba.











