Ana zargin wani da yunkurin hallaka tsohuwar matarsa

'Yan sanda sun cafke mutumin, jim kadan bayan an garzaya da matar asibiti cikin mawuyacin hali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun kama mutumin jim kadan bayan an garzaya da matar asibiti cikin mawuyacin hali

'Yan sandan kasar Nicaragua sun kama wani mutum, da ake zargi da yunkurin hallaka tsohuwar matarsa ta hanyar bata wata guba da ake amfani da ita don kashe kwari a gona.

An dai tsare mutumin bayan an garzaya da matar asibiti, wadda ta shiga mawuyacin hali sakamakon gubar Alminium Phosphide da tsohon mijin nata ya yi.

'Yan uwan matar sun yi kirarin an dura mata gubar ne a lokacin da tsohon mjin na ta ke jima'i da ita ta hanyar yi mata fyade da dama can ya saba aikatawa a lokacin da suke da aure.

Lamarin ya fusata mata a Nicaragua, masu rajin kare hakkin mata sun yi kira ga gwamnati ta kara daukar tsauraran matakai kan cin zarafin mata.

Karanta karin labarai