MDD na son Saudiyya ta saukaka wa mata tafiya da muharrami

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kare hakkin mata ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga hukumomin Saudiyya, da su cire haramcin barin mata gudanar da harkokin rayuwa ciki har da yin tafiye-tafiye ba tare da muharraminsu ba.
Wata doka da Majalisar ke ganin kungiyoyin kare hakkin matan na son bijirowa Saudiyyar a shekarar da ta wuce, ta ce zai fi wa matan kasar sauki idan suka samu amincewar gwamnati a kan wani abu da ya shafi rayuwarsu, maimakon sanya muharramansu, sai dai har yanzu ana ci gaba da amfani da tsohuwar dokar a kasar.
To sai dai kuma sauye-sauyen da yarima Muhammad bin Salman, ya fara a kasar, mata sun fara samun 'yancin zuwa kallon wasanni a filin wasa da ke kasar, sannan an dage haramcin tuka mota a gare su.
Kazalika matakin daukar mata a aikin soja na cikin sauye-sauyen da kasar ke gudanarwa a watannin baya-bayan nan, domin inganta damar mata a kasar da ake yi mata kallon mai cike da 'tsattsauran ra'ayi.







