An yi barazanar kai wa Saudiyya hari

'Yan tawayen Houthi sun batawa Saudiyya rai

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yan tawayen Houthi sun batawa Saudiyya rai

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun yi barazanar kai hari tsakiyar kasar Saudiyya saboda ci gaban da take yi na hana shiga da kayan masarufi kasar.

Shugaban 'yan tawayen Abdulmalik al-Houthi ya ce dakarunsa sun san yadda za su kai harin da zai yi mummunar barna a Saudiyya.

Kwanakin baya ne mayakan 'yan tawayen Houthi suka harba makami mai linzamin da ya doshi birnin Riyadh.

Lamarin ya yi matukar bata ran Saudiyya abin da ya sa ta tsaurara matakin hana shugaba arewacin Yemen da ke hannun 'yan tawaye.

Sai dai an dan sassauta matakin.

Miliyoyin 'yan kasar Yemen ke fuskantar masifar yunwa kuma kasashen duniya na ci gaba da matsa lamba kan Saudiyya ta janye matsin da take yi wa Yemen.