Nigeria: Sojoji sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Magumeri

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sun fatattaki 'yan Boko Haram daga garin Magumeri na jihar Borno bayan sun kwashe lokaci mai tsawo suna fafatawa da su.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutanen garin Magumeri sun shaida masa ta wayar salula cewa sun arce zuwa wani daji da ke kusa da su.
Sai dai rundunar sojin kasar ta musanta cewa an kwace garin daga farko.
Amma sojin sun ce sun kwashe lokaci mai tsawo suna gumurzu da mayakan kafin su fatattake su daga bisani, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku da kuma jikkata shida.
A farkon watan da mu ke ciki ne,aka kashe mutum shida tare da kone gidaje masu yawa a harin da aka kai garin .
Mayakan Boko Haram sun kara zafafa hare haren da suke kai wa tun bayan daukewar ruwan sama a watan Satumba.
Wannan shi ne hari na baya bayanan tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a jihar Adamawa, inda mutum 50 suka hallaka.
Harin na cikin hare hare mafi ya muni da aka kai tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a shekarar 2015, inda ya yi alkawarin kawo karshen masu tada kayar baya.











