Ma'auratan da aka yi garkuwa da su shekara biyar sun kubuta

An saki wasu ma'aurata 'yan yankin Arewacin Amurka, da wata kungiya mai alaka da Taliban ta sace su a Afghanistan, shekara biyar da ta wuce.
Mista Joshua Boyle, dan asalin Canada ne, ya yin da matarsa mai suna Caitlan Coleman, ta fito daga Amurka.
Ma'auratan sun haifi 'ya'ya uku a lokacin da ake tsare da su.
An sace ma'auratan ne jim kadan bayan sun yi aure a Afghanistan.
Bayan sace su, sun dauki lokuta su na aiko da hotunansu da kuma wasiku, amma daga bisani sai aka ji shiru, sai a watan Disambar bara ne suka aiko da hoton bidiyonsu da kuma 'ya'yan da suka haifa a lokacin da suke tsare, kuma a lokacin ne su ka yi bayanin halin da su ka tsinci kansu ciki tun daga lokacin da aka tsare su.
To tun daga wannan lokaci kuma su kai dib, sai a makon daya gabata ne aka kubutar da su.
An dai samu damar kubutar da su ne a Pakistan, bayan da wadanda suka sace sun su ka dauko su daga inda aka ajiye su, su ka kawo su inda aka sake su tare da 'ya'yan nasu.







