'Masu teba na iya kamuwa da shanyewar barin jiki'

Masana kimiyya a Birtaniya sun nuna shakku a kan bayanan da ke cewa wasu masu teba za su iya kasancewa suna da jiki da kuma lafiya.

Binciken da aka gudanar a baya sun nuna cewa a duk kaso daya cikin uku na masu teba suna da lafiya, kuma ba su da hawan jini da kuma yawan maiko a jikinsu.

To sai dai kuma masu bincike a jami'ar Birmingham sun gano cewa yawan maiko a jikin mutum na kara hadarin kamuwa da cutukan da suka shafi zuciya da shanyewar barin jiki.

An yi wannan binciken ne a kan mutane miliyan uku da rabi a cikin shekaru ashirin.