Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Qatar 2022 - Jadawali da sakamakon wasannin Kofin Duniya
Wannan shafi zai dinga sabunta kansa da zarar an fara gasar
A ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba za a take gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar da ke Gabas ta Tsakiya.
Tawagar ƙasashe 32 ne ke fafatawa a gasar da za a yi karo na 22 a tarihi, kuma karon farko da ake yin ta a wata ƙasar Larabawa.
Ƙasashen Afirka a gasar su ne Ghana da Senegal da Kamaru da Moroko da Tunisiya.
Faransa ce mai riƙe da kofin bayan ta lashe shi a gasar da aka yi a Rasha a shekarar 2018.