Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kylian Mbappe: Ɗan wasan gaban Faransa zai sabunta yarjejeniyarsa da Paris St-Germain
Ɗan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe ya sake cimma yarjejeniya da ƙungiyar don tsawaita zamansa.
An sha alaƙanta ɗan wasan mai shekara 23 da ya lashe Kofin Duniya a 2018 da komawa Real Madrid, ama yanzu ya amince ya tsawaita zamansa a birnin Paris tare da zakarun Ligue 1.
Mbappae zai sanya hannu kan yarjejeniya mai gwaɓi ta tsawon shekara uku a PSG.
Har yanzu bai saka hannu kan yarjejeniyar ba amma ana ganin PSG za ta sanar da hakan yayin da suke buga wasan ƙarshe da Metz a yammacin Asabar.
A cewar ƙwararre kan gasar La Liga, Guillem Balague, a wata da ya gabata PSG ta shirya tsaf don ba wa dan wasan yuro miliyan 150 a matsayin albashi don ta hana shi zuwa Madrid.
A watan da ya gabata ɗin ne kuma Mbappe ya ƙulla alƙawari da Real kan albashinsa game da komawar tasa amma daga baya ya sauya ra'ayi.
Tun farko ya koma PSG a matsayin aro daga Monaco a Agustan 2017, inda ya taimaka musu suka lashe gasar Ligue 1 huɗu da kaka biyar.
PSG ta ƙagu ya ci gaba da murza mata leda, har ma suka yi niyyar biyan sa yuro miliyan 21 duk shekara.
'Abin da PSG ta yi cin fuska ne ga ƙwallon ƙafa'
Shugaban gasar La Liga ta Spaniya, Javier Tebas, ya caccaki PSG da mamallakin ƙungiyar ɗan ƙasar Qatar, Nasser Al-Khelaifi, game da sabon kwantaragin da suka ba wa Mbappe na miliyoyin kuɗi.
Cikin wani saƙon Twitter, Tebas ya ce: "Abin da PSG ke son yi da ba wa Mbappe wannan maƙudan kuɗin bayan ta sanar da asarar miliyan yuro 700 a 'yan shekarun nan kuma tana da ƙunshin albashi [da take biya] na yuro miliyan 600, cin fuska ne ga ƙwallon ƙafa."
A cewar wani rahoto da wata hukumar Ligue ta wallafa a watannan mai suna Ligue de Football Professionel (LFP), PSG ta yi asarar yuro miliyan 224.3 a kakar 2020-21.
Hakan ta faru ne bayan asarar yuro miliyan 124.2 a kakar 2019-20 sakamakon annobar korona bayan an katse gasar ta Ligue 1 a watan Maris na 2020.