Yakin Ukraine: Tawagar Amurka za ta je ziyarar gani da ido Ukraine

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya sanar da cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken da na harkokin tsaro, Lloyd Austin za su ziyarci birnin Kyiv a wannan Lahadin.

Mista Zelensky ya ce yana sa ran su iso kasarsa da kayayyakin taimako da Ukraine ke ta roko a kai.

Ya kuma sanar da cewa kusan mutane rabin miliyan - da suka hada da yara akalla dubu biyar - an maido su daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye zuwa yankin Rasha.

Mista Zelensky ya kuma soki ganawar da sakataren janar na MDD, Antonio Guterres, zai yi da Vladimir Putin a Moscow a ranar Talata kafin ya je Kyiv.

Ya ce kamata ya yi Mista Guterres ya soma zuwa Ukraine domin ganin abubuwa da idonsa kafin ya je Rasha.

Mista Zelensky ya shafe sa'o'i uku yana jawabi ga manema labarai daga tashar jirgi ta karkashin kasa a Kyiv. Har aka hango ya ɗan dakatar da jawabi lokacin da jirgin kasa ya zo wucewa.

Rasha na cigaba da luguden-wuta

Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya yi Allah-wadai da harin makami mai linzami da Rasha ta kai a rukunni gidajen mutane da ke kusa da tashar jirgin ruwa ta Odesa, mutum 8 suka mutu.

Gwamnan Luhansk da ke gabashin kasar, Sergiy Gayday, ya ce fararan-hula shida suka mutu a luguden wuta da Rasha tayi kan wani kauye, Girske.

Ya ce, "suna tada bama-bamai a ko ina da kashe kowa da makaman artilary da hare-haren rokoki, ba dare ba rana. Idan ka samu dama to kawai ka tsere, muna ta aiki da kungiyoyi domin ceto rai".

Kungiyar tsaro da hadin kai a Turai tace akwai masu sa ido kan ayyukan sojin kasa da kasa da dama da aka garkame a gabashin Ukraine.

Kungiyar ta nuna damuwa kan yada tace an hana ma'aikatanta 'yanci a Donetsk da Luhansk.

A ranar Juma'a Kungiyar ta Burtaniya, ke cewa dakarun Rasha sun tsare wasu daga cikin ma'aikatanta..