Ajax tana ta kokarin hana Erik ten Hag komawa Man United

Ajax tana yin dukkan abin da ya da ce don hana Erik ten Hag komawa Manchester United in ji jami'in kungiyar Gerry Hamstra.

Manchester United na daf da tabbatar da nada Teb Had a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar kaka uku.

Ajax ta yi rashin Dutch Cup 2-1 a hannun PSV Eindhoven ranar Lahadi.

''Mun so ya ci gaba da aiki tare da kungiyarmu. Amma har yanzu ba mu fitar da tsammani ba, tunda har yanzu bai barmu ba,'' kamar yadda Hamstra ya sanar da EPSN tun kan su yi rashin nasarar ranar Lahadi.

Ajax ce kan gaba a gasar Netherlands da tazarar maki hudu tsakaninta da PSV, bayan da take shirin lashe kofi na uku karkashin Ten Hag.

''Ana ta zawarcin Erik ten Hag wannan ba komai bane. Ya nuna kwarewarsa,'' kamar yadda Hamstra ya sanar ranar Lahadi.

''Muna ta kokarin ganin ya ci gaba da horar da Ajax, abin da muke kai kenan a yanzu.

''Sai dai mun kwan da sanin cewar watakila Ten Hag ya tsaya, ko kuma ya koma United.''