Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City 2-2 Liverpool: An raba maki tsakanin Man City da Liverpool
Manchester City da Liverpool sun raba maki a tsakaninsu, bayan da suka tashi 2-2 a wasan mako na 32 a gasar Premier League da suka kara a Etihad ranar Lahadi.
Minti biyar da fara tamaula Kevin de Bruyne ya ci wa City kwallo, daga baya Liverpool ta farke ta hannun Diego Jota.
To sai dai kuma City ta kara na biyu ta hannun Gabriel Jesus a minti na 36, haka nan ma Liverpool ta farke ta hannun Sadio Mane.
Wannan shine karon farko da City ta fara cin kwallo aka farke ta kuma raba maki da wata kungiya a bana, a baya idan ta fara cin kwallo, sai dai ta tashi da maki ukun.
Teburin Premier League
Karo na 23 da aka kece raini tsakanin Pep Guardiola da Jurgen Klopp a matakin masu horar da tamaula, kowanne ya ci takwas da canjaras na bakwai kenan,
Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana, tana nan a matakinta na biyu a teburin Premier League, wadda ta lashe Caraboa Cup na kakar nan,
Ita kuwa City ta ci gaba jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, za kuma ta ziyarci Atletico Madrid a wasa na biyu a Quarter finals ranar 13 ga watan Afirilu.
City ta yi nasarar cin Atletico Madrid 1-0 a wasan farko a daf da na kusa da na karshe da suka fafata a Etihad ranar Talata 5 ga watan Afirilu.
Liverpool kuwa za ta karbi bakuncin Benfica a Anfield ranar 13 ga watan Afirilu, bayan da kungiyar Anfield ta ci 3-1 a Portugal ranar Talata 5 ga watan Afirilu.
Ranar 16 ga watan Afirilu Manchester City da Liverpool za su sake karawa a tsakaninsu a gasar FA Cup.