Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Modric na sansana Man City, Barca da Bayern na takarar zawarcin Boubacar Kamara
Dan wasan Real Madrid, Luca Modric mai shekara 36, na sha'awar zuwa Manchester City idan kwantaraginsa ya kare da kulob din a lokacin bazara.
Newcastle da Roma na rige-rigen sayen dan wasan Hoffenheim dan asalin kasar Austria, Florian Grillitch mai shekara 26n, a watan Janairu lokacin da za a bude kasuwar musayar 'yan wasa.
Bayern Munich da Barcelona na idan-ba-ka-yi ban wuri wajen zawarcin dan wasan Marseille dan kasar Faransa, mai shekaru 22 Boubacar Kamara.
Shi kuwa Ousmane Dembele wanda shi ma dan kasar ta Faransa ne ya yi watsi da tayin tsawaita masa kwantaraginsa da Barcelona ta yi, inda hakan ke nuni da cewa dan wasan mai shekaru 24 ya shirya zaman kansa.
Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya gana da darektan kwallo na Barcelona, Mateu Alemany da shugaban kulob din Ferran Reverter kan a lokacin wani cin abincin dare, inda daya daga cikin batutuwan da suka tattauna suka hada da yadda rayuwar dan wasan gaba, mai shekara 21, Ferran Torres.
Idan dai har Torres ya koma Barcelona, hakan ka iya bude kofa ga dan wasan RB Leipzig mai shekaru 23, Dani Olmo zuwa ga Manchester City.
Har wa yau, Manchester City din dai na duba yiwuwar sayen dan wasan da zai rinka ci mata kwala-kwalai, a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa da za a bude a watan Janairu.
Shi ma tsohon dan wasan baya na Aston Villa, Kevin Phillips ya yi amannar cewa tsohon kulob din nasa ya kamata ya cefanar da Anwar El Ghazi mai shekara 26, maimakon dan kasar Burkina Faso, Bertrand Traore mai shekara 26 a watan Janairu lokacin bude kasuwar musayar 'yan wasa.