Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trabzonspor 1-2 Roma: Jose Mourinho ya fara jan ragama da kafar dama
Jose Mourinho ya fara da jan Roma da kafar dama, bayan da ya je Turkiya ya ci Trabzonspor a wasan neman gurbin shiga sabuwar gasar Europa Conference League.
A wasan farko da suka buga, kyaftin din Roma, Lorenzo Pellegrini ne ya fara cin kwallo, bayan da Henrikh Mkhitaryan ya buga masa tamaular.
Sai dai kuma Trabzonspor ta farke ta hannun Andreas Cornelius, wanda ya shiga karawar daga baya.
Daga baya Roma ta kara na biyu ta hannun Eldor Shomurodov a wasan farko da ya buga wa kungiyar, wadda ta sayo shi daga Genoa.
Roma za ta kai zagayen raba rukunin gasa ta uku ta Turai, idan har ta kara a zagaye na biyu ba a doke ta ba ranar Alhamis 26 ga watan Agusta a Stadio Olimpico.
Mourinho tsohon kocin Chelsea da Manchester United da kuma Tottenham ya maye gurbin Paulo Fonseca a Roma, bayan kammala kakar bara.
Roma za ta fafata da Fiorentina a wasan makon farko na bude gasar Serie A ta bana ranar Lahadi.