Ahmed Musa yana dab da komawa kungiyar Kano Pillars

    • Marubuci, Daga Oluwashina Okeleji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Football Writer, Nigeria

Kyaftin din kungiyar kwallon kafar Super Eagels Ahmed Musa yana dab da sanya hannu domin murza tamaula a tsohuwar kungiyarsa, Kano Pillars, a wani mataki na karfafa gwiwar kungiyoyin da ke gasar lig-lig a Najeriya.

Dan wasan mai shekara 28, wanda ba ya buga wa kowacce kungiya tamaula tun da ya bar Al Nassr ta Saudiyya a watan Oktoba, ya samu tayin tafiya Ingila da Rasha da kuma Turkiyya.

Sai dai a yayin da yake nazari kan matakin da zai dauka na tafiya wata kasar Turai a bazara, dan wasan ya karbi goron gayyata daga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Shehu Dikko, shugaban League Management Company (LMC) domin ya murza leda a Pillars.

Tsogon dan wasan na Leicester City ya shaida wa BBC Sport Africa. cewa: "Bayan na yi magana da gwamna da shugaban LMC ina duba yiwuwar murza tamaula a Kano pillars."

"Zan yi duk abin da zai fito da mutuncin kwallon kafar Najeriya kuma ina kallon Kano Pillars da matukar muhimmanci.

"Ita ce kungiyar da ta taimaka mini na zama shahararren dan wasan kwallon kafa a yau, don haka wannan dangantaka ta wuce ta kwallon kafa danganaka ce mai yauki."

Wata majiya da ke kusa da kungiyar ta shaida wa BBC Sport Africa ana dab da kammala kulla yarjejeniyar dawo da Musa Kano Pillars.

Musa, wanda ya bude gidajen koyon kwalon kafa da atisaye biyu a arewacin Najeriya, ya ci wa Kano Pillars kwallaye 18 lamarin da ya sa ta yi nasarar lashe kofin lig na Najeriya a kakar wasan 2009/10.

Musa ya buga wa Najeriya kwallo sau his 96 inda a wasansu na baya bayan nan Super Eagles ta doke Lesotho da ci 3-0 a birnin Lagos inda ta samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka.

Nasarorin da ya samu a Rasha da Saudiyya

Musa ya zura kwallaye 11 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 14a wasanni 57 da ya buga wa Al Nassr, tun da ya koma can daga Leicester City a bazarar 2018, abin da ya sa suka lashe kofunan Saudi Pro League da Super Cup.

Kazalika ya yi nasara a Rasha lokacin da ya murza leda a CSKA Moscow inda ya lashe kofunan lig-lig guda uku da kuma kananan kofuna uku, kafin ya tafi Leicester City a watan Yulin 2016.

Musa ya gaza taka rawar gani a Leicester inda ya ci mata kwallaye biyar a wasanni 33.

Duk da yake West Brom ta kasa daukarsa saboda batun kudi, ana rade-radin cewa Musa zai koma Firimiya Lig ta Ingila ko CSKA Moscow, inda ake matukar girmama shi saboda kwallaye 61 da ya ci mata sanna ya taimaka aka ci kwallaye 33 a wasanni 184 da ya buga.