Martin Odegaard ya koma Arsenal domin buga matawasannin aro zuwa karshen kakar bana daga Real Madrid.

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan dan kasar Norway mai shekara 22, ya koma kungiyar Arsenal ne bayan da Mesut Ozil ya koma taka leda a Fenebahce ta Turkiya.
Odegaard ya nemi izinin barin Real Madrid a watan Janairu ganin ba a saka shi a wasa da yawa a kakar bana.
Wasa tara ya buga wa kungiyar har da bakawi a La Liga, kuma ba a yi minti 90 da shi ba a cikin filin tamaula tun bayanda ya koma Real Madrid daga Real Sociedad wadda ya bugawa wasannin aro.
Real Sociedad ta bukaci dan kwallon ya sake buga matawasannin aro, ita kuwa Real Madrid ta zabi ya koma taka ledaa Ingila domin ya kara samun gogewa.
Riga mai lamba nawa Arsenal ta bai wa Odegaard?
Odegaard wanda ya saka riga mai lamba 21 a Real Madrid yakarbi mai lamba 11 a Gunners da zai yi wasa zuwa karshenkakar bana.
Fittattun 'yan wasan Arsenal da suka sa riga mai lamba 11 sun hada da Marc Overmars da Robin van Persie da Ozil, wandadaga baya aka bashi lamba 10.
Yaushe ne Odegaard zai fara yi wa Arsenal wasa?
Watakila Odegaard ya buga wa Arsenal gasar Premier League da za ta yi da Manchester United a Emirates ranar Asabar.
Ya rage idan dan kwallon yana kan ganiya, kuma idan koci yayanke shawarar ya fara wasan da shi ko sai daga baya ya yicanji ko kuma ya yi zaman benci gaba daya.
Bayan wasan da Gunners za ta yi da Manchester United zakuma ta ziyarci Molineux domin fafatawa da Wolverhampton ranar 2 ga watan Fabrairu, watakila ya fara wasa a ranar.
Ko zai buga Europa League kuwa?
Odegaard ya cancanci buga wa Arsenal Europa League za ta iya saka sunansa cikin masu buga mata gasar.
Arsenal za ta kara da Benfica a wasannin kungiyoyi 32 da suka rage a gasar a cikin watan Fabrairu.
Arsenal wadda ta doke Southampton da ci 3-1 ranar Talata ta koma ta takwas a kan teburin Premier League da maki 30.











