Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallo: Sancho, Pochettino, Alli, Eriksen, Christie, Ozil, Modric Ramos
Manchester United ta haƙiƙance cewa za ta sayi ɗan wasan Ingila daga Dortmund mai shekara 20, Jadon Sancho, kan kuɗi ƙasa da fan miliyan 100 a wannan shekarar. (90 Min)
Arsenal ta bi sahun sauran ƙungiyoyi wurin neman Ryan Christie mai shekara 25 daga ƙungiyar Celtic kuma tana fatan tsohon abokin wasansa Kieran Tierney zai lallaɓa shi ya koma Emirates da taka leda. (90 Min)
A gefe guda kuma, kocin Arsenal ɗin Mikel Arteta ba shi da tabbas ko Mesut Ozil zai koma cikin babbar tawagar ƙungiyar. Ozil bai buga wasa ko ɗaya ba a kakar bana. (Sky Sports)
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya musanta rahotannin cewa Luka Modric mai shekara 35 da Sergio Ramos mai 34 da Lucas Vazquez mai 29 za su bar ƙungiyar. (Team Talk)
Ana alaƙanta sabon kocin PSG, Mauricio Pochettino, da tsoffin 'yan wasansa a Tottehnham wato Dele Alli mai shekara 24 da kuma Christian Eriksen mai shekara 28, wanda ke Inter Milan a yanzu. (AS)
Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce "abin mamaki ne" idan aka ga sun sayi wani ɗan wasa a Janairu kuma ba zai nemi shugaban ƙungiyar ba Daniel Levy ya saya masa wani sabon ɗan wasa. (Standard)
Borussia Dortmund na son matashin ɗan wasan gefe na Manchester City, Jayden Braaf mai shekara 18. (Bild, via Mail)