Jacques Anouma zai yi takarar kujerar shugaban kwallon Afirka

Dan kasar Ivory Coast, Jacques Anouma zai tsaya takarar shugabancin kujerar hukumar kwallon kafar Afirka a zaben da za a yi a watan Maris.

Anouma wanda hukumar kwallon kafar kasarsa ta amince ya shiga takarar - ya taba bayyana aniyarsa shekara bakwai da suka wuce.

Mai shekara 68, shi ne na biyu da ya sanar da zai yi takara ranar Alhamis, bayan shugaba mai ci Ahmad, wanda ya sanar da son yin tazarce a watan jiya.

Ranar Asabar hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ta bayyana goyon bayanta ga Anouma tsohon mamba a kwamitin amintattu na Fifa kan takarar da zai yi.

Duk dan takarar dake son shiga zaben da za a yi na shugaban CAF cikin watan Maris a Morocco zai kasance wanda hukumar kwallon kafar kasarsa ta amince da shi.

Anouma ya ja ragamar shugabancin hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast tsakanin 2002 da 2011.

Ya kuma zama mamba a kwamitin amintattu na hukumar kwallon kafar Afirka tsakanin 2007 da kuma 2015.