Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Erling Braut Haaland: Ya ci kwallo 26 a wasa 28 da ya yi wa Dortmund
Erling Braut Haaland ya zura wa Borussia Dortmund kwallo 26 a wasa 28 da ya buga mata a dukkan fafatawa.
Mai shekara 20 ya zura biyu a ragar Club Brudge a Gasar Champions League da Dortmund ta yi nasara da ci 3-0 ranar Laraba.
A wasan na rukuni na shida da suka fafata a Belgium, Thorgan Hazard ne ya fara cin kwallo a minti na 14 da fara wasa. sannan Haaland ya ci biyun.
Dan wasan wanda ya koma kungiyar ta Jamus a Janairun 2020 ya ci kwallo 14 a wasa 11 da ya yi a Champions League.
Haaland ya yi wannan bajintar ta cin kwallaye da yawa a wasa kadan a Gasar Zakarun Turai, kuma Harry Kane ne ya fara cin 14.
Haland dan kwallon tawagar Norway ya ci kwallo a dukkan kungiyoyi bakwai da ya fuskanta a Gasar ta Zakarun Turai.
Dortmund tana ta daya a rukuni na shida da maki shida da tazarar maki daya tsakaninta da Lazio mai biye da ita.
Ranar 7 ga watan Nuwamba Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan Gasar Bundesliga.
Dortmund tana ta biyu a teburin Bundesliga da maki 15 iri daya da na Bayern Munich wacce take jan ragamar teburin.