Man United vs Chelsea: United na fatan cin wasan farko a gida a bana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Manchester United za ta karbi bakuncin Chelsea ranar Asabar a Gasar cin Kofin Premier League karawar mako na shida a Old Trafford.
Idan har United ta yi nasara a wasan shi ne na farko da kungiyar ta yi a gida a kakar bana, kuma za ta hau kan Chelsea a gasar Premier League.
Ita kuwa Chelsea na fatan buga wasa hudu a jere a Premier League ba tare da an doke ta ba.
Idan har Chelsea ta ci United a Old Trafford shi ne na farko da ta yi wannan bajintar tun watan Mayun 2013.
Chelsea tana mataki na takwas a teburin Premier League, bayan wasa biyar da cin biyu da rashin nasara a biyu da canjaras daya da makinta takwas.
Ita kuwa United mai maki shida tana matsayi na 15 a kasan teburi, bayan karawa hudu da nasara a biyu aka doke ta fafatawa biyu.
Sakamakon wasannin da kungiyoyin suka fafata a 2019/2020
Lahadi 11 ga watan Agustan 2019 Premier League
- Man Utd 4 - 0 Chelsea
Laraba 30 ga watan Oktoban 2019 Carabao Cup
- Chelsea1 - 2 Man Utd
Litinin 17 ga watan Fabrairun 2020 Premier League
- Chelsea 0 - 2 Man Utd
Ranar Lahadi 19 ga watan Yulin 2020 FA Cup
- Man Utd1 - 3 Chelsea
A wasa 56 da kungiyoyin suka fafata a tsakaninsu, United ta yi nasara a 17, Chelsea ta ci 18 da canjaras 21.
Ko kun san?
Manchester United na neman doke Chelsea sai uku a jere a karon farko a Gasar Premier League.
Watakila Marcus Rashford ya zama dan wasan Manchester United na farko da zai ci Chelsea kwallo biyu ko fiye da haka a Gasar Premier League biyu a jere.
Idan har Edison Cavani ya buga wa United wasan, zai iya zama na biyu mai yawan shekaru da ya fara wasan Premier balle ya ci kwallo a wasan yana da shekara 33 da kwana 253.
Wanda ya fara yin bajintar shi ne Zlatan Ibrahimovic da ya ci wa Manchester United kwallo a Agustan 2019 yana da shekara 34 da kwana 316.
Tun daga kakar bara a Gasar ta Premier League, Chelsea ta ci kwallo 87 da zura 42 a raga a wasannin da ta fafata a waje.
United ta yi nasarar doke Paris St German 2-1 a gasar Champions League a Faransa ranar Talata 20 ga watan Oktoba.
Ita kuwa Chelsea ta tashi 0-0 a wasan da ta buga da Sevilla a Stamford Bridge.
Wadanda za su yi alkalanci

Asalin hoton, Getty Images
Alkalin wasa: Martin Atkinson. Mataimakansa: Lee Betts da Constantine da kuma Hatzidakis.
Mai jiran ko ta kwana: Jonathan Moss.
Mai kula da VAR: Stuart Attwell. Mataimakinsa: Simon Long.
Wasanni biyar nan gaba da United za ta buga:
Laraba 28 ga watan Oktoba Champions League
- Man Utd da RB Leipzig
1 ga watan Nuwamba Premier League
- Man Utd da Arsenal
Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League
- Basaksehir da Man Utd
Asabar 7 ga watan Nuwamba Premier League
- Everton da Man Utd
21 ga watan Nuwamba Premier League
- Man Utd da West Brom
Wasanni biyar da Chelsea za ta kara nan gaba:
Laraba 28 ga watan Oktoba Champions League
- FK Krasnodar da Chelsea
31 ga watan Oktoba Premier League
- Burnley da Chelsea
Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League
- Chelsea da Rennes
7 ga watan Nuwamba Premier League
- Chelsea da Sheff Utd
21 ga watan Nuwamba Premier League
- Newcastle da Chelsea
Wasannin mako na shida da za a buga a gasar Premier League
Juma'a 23 ga watan Oktoba
- Aston Villa da Leeds United
Asabar 24 ga watan Oktoba
- West Ham United da Manchester City
- Fulham da Crystal Palace
- Manchester United da Chelsea
- Liverpool da Sheffield United
Lahadi 25 ga watan Oktoba
- FC Southampton da Everton
- Wolverhampton Wanderers da Newcastle United
- Arsenal da Leicester City
Litinin 26 ga watan Oktoba
- Brighton & Hove Albion da West Bromwich Albion
- Burnley da Tottenham











