Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Sancho, Traore, Gomes, Dybala

An cehar yanzu Manchester United za ta iya samun damar daukar dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, bayan ta gaza daukarsa a bazara. (Star)

KazalikaUnited na yunkurin daukar dan wasan Sporting Lisbon mai shekara 16 Luis Gomes. Ana yi wa dan wasan na Portugal lakabi da suna 'Luis Figo' na nan gaba a kasarsa. (Mirror)

Dan wasan Wolves Adama Traore, mai shekara 24, zai yi watsi da tayin tafiya Barcelona ko Liverpool domin ya sanya hannu a sabuwar kwangilar da zai rika karbar £100,000 duk mako a Molineux. Dan wasan na Sufaniya ya koma kungiyar ne daga Middlesbrough a 2018. (Sun)

Tsohon dan wasan Liverpool Jamie Carragher ya ce dole kungiyar ta dauko sabon dan wasan baya don maye gurbin dan wasan Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 29, wanda ya ji rauni a wasansu da Everton. (Mail)

Ranar Litinin Wayne Rooney, mai shekara 34, yake sa ran sanin sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar korona zai fito bayan an gano cewa wani abokinsa wanda ya sayar masa agogo ya kamu da cutar. (Daily Telegraph - subscription required)

Dan wasa Argentina Paulo Dybala, mai shekara 26, ya yi cacar baki da baban jami'in kwallon kafar Juventus Fabio Paratici bayan da aka cire shi daga tawagar farko da ta murza leda ranar Asabar. (Mail via Tuttosport)

Dan wasan Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekara 23, ya zama daya daga cikin 'yan kwallon Newcastle da ya fi samun kudi bayan ya kulla sabuwar yarjejeniyar shekara shida da kungiyarl - inda za a kusan ninka alawus din na mako wato £70,000. (Newcastle Chronicle)

Dan wasan Liverpool Harvey Elliott, mai shekara 17, ya yi nazari kan tawagar Blackburn kafin ya amince ya tafi zaman aro a kungiyar. (Mail)

Kungiyoyin da ke buga gasar EFL sun yi barazanar kin biyan haraji a yunkurin samun tallafin gwamnati. (Sun).