Ciwon da Virgil van Dijk ya ji mai muni ne in ji Klopp, bayan karawa da Everton

Raunin da mai tsaron bayan Liverpool, Virgil van Dijk' ya ji a gwiwar kafarsa mai muni ne in ji koci Jurgen Klopp.

Van Dijk ya ji raunin ne a karo da ya yi da mai tsaron ragar Everton, Jordan Pickford tun kan hutu a wasan da Liverpool ta tashi 2-2 ranar Asabar a gasar Premier League.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Netherlands mai shekara 29 na jiran wani kwararren litita da zai auna girman raunin.

"Virgil ya yi wasanni da dama ban san iyakarsu ba a jere, yana kuma jin radadi, amma yanzu ba zai iya ci gaba ba," in ji Klopp.

Liverpool ta yi korafin samun fenariti a lokacin da alkain wasan bai yi wani ba, bayan da aka ce Van Dijk ya yi satar gida, kafin mai tsaron ragar Ingila, Pickford ya gurje masa kafa.

''Na gani karara fenariti muka samu na kuma ga mataimakin alkalin wasa ya daga tuta sama, na kuma dauka za a je a duba laifin amma hakan bai yi yu wa ba. '' in ji Klopp.

''Ba zan ce Jordan Pickford ya yi laifin da gangan ba, amma bai kamata mai tsaron raga ya yi wani abu irin haka a cikin da'irarsa ba.