Thomas Partey: Arsenal ta sayi ɗan wasan Atletico Madrid a kan £45m

Thomas Partey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Thomas Partey na cikin tawagar Atletico Madrid da ta taka rawar gani a gasar Zakarun Turai ta 2015-16

Arsenal ta kammala sayen Thomas Partey daga Atletico Madrid a kwangilar tsawon lokaci bayan ta biya euro 50m (£45.3m) kudin darajar dan wasa.

Dan kasar Ghana mai shekara 27 ya buga wasan lig 35 kuma ya ci kwallaye uku a Atletico a yayin da suka kammala gasar La Liga da ta wuce a matsayi na uku.

Ya buga wa Atletico wasa sau 188 tun da ya je kungiyar a 2011.

Shi kuma dan wasan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, ya tafi Atletico inda zai yi zaman aro a kungiyar da ke buga gasar La Liga.

An dade ana rade radin cewa Arsenal za ta dauko Partey, wanda yi zarra sau 29 a kwallon duniya.

Partey ya yi nasarar daukar Kofin Europa League na 2017-18 da kuma 2018 Super Cup a Atletico kuma ya sanya hannu kan sabuwar kwangila a Wanda Metropolitano a 2018, zuwa karshen watan Yunin 2023.

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce: "Mun dade muna sa ido a kan Thomas, don haka yanzu muna farin cikin daukar dan wasa mai kyau a tawagarmu.

"Dan wasan tsakiya ne mai matukar basira da kazar-kazar. Zai yi amfani da kwarewarsa da ya samu daga babar kungiya wadda ta fafata a kololuwar Gasar La Liga da Gasar Zakarun Turai a shekaru da dama."

Arsenal ta so daukar dan wasan tsakiyar Lyon Houssem Aouar, mai shekara 22 - sai dai Aouar ya shaida wa gidan talbijin na Faransa ranar Litinin kafin rufe kasuwar 'yan kwallo cewa zai ci gaba da murza leda a kungiyar da ke buga gasar Ligue 1.