Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Guendouzi, Emerson, Partey, Diallo, Todibo, Skriniar, Cullen

Matteo Guendouzi

Asalin hoton, AFP

Dan wasanArsenal Matteo Guendouzi, mai shekara 21, yana shirin tafiya Hertha Berlinda ke buga gasar Bundesliga, bayan ya samu matsala da Emirates Stadium. (Mirror)

Tottenham za ta yi yunkurin karshe domin dauko dan wasan Inter Milan mai shekara 25 dan kasar Slovakia Milan Skriniar. (Mirror)

Juventus na shirin karbo aron dan wasan Chelsea dan kasar Italiya mai shekara 26, Emerson Palmieri. (Calciomercato - in Italian)

Arsenal ta karaya a kokarinta na dauko dan wasa Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, dagaAtletico Madrid. Kungiyar ta ce ba za ta iya biyan kudin darajar dan wasan £45m da aka sanya a kansa ba. (Mirror)

Dan wasan Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 20, zai iya kama hanyarsa ta barin Barcelona domin tafiya zaman aro, inda aka ce ya fi son zuwa Fulham, ko da yake Everton ta bayyana sha'awar daukarsa. (Le 10 Sport - in French)

Bayern Munich za ta mayar da hankali wurin dauko dan wasan Juventus da Brazil Douglas Costa, mai shekara 30, idan ta kasa dauko dan wasanChelsea dan kasar Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 19. (Kicker - in German)

Celtic na sha'awar dauko dan wasanWest Ham dan yankin Scotland Robert Snodgrass, mai shekara 33, domin ya yi zaman aro ko da yake za ta iya sayensa. (Sun)

An kammala yarjejeniyar tafiyar dan wasan Antonio Rudiger AC Milan domin yin zaman aro, indaChelsea take cike da farin cikin barin dan wasan mai shekara 27 ya tafi kafin ta tattauna kan tsawaita zamansa, inda saura shekara biyu kwangilarsa ta kare. (90min)

Anderlecht na dab da kammala kulla yarjejeniya da dan wasan West Ham dan yankin Jamhuriyar Ireland Josh Cullen, mai shekara 24. (Het Laatste Nieuws - in Dutch)

Dan wasan Roma da Netherlands Justin Kluivert, mai shekara 21, yana kan hanyarsa ta zuwa RB Leipzig domin yin zaman aron kakar wasa daya. (Fabrizio Romano via Football Italia)

Paris St-Germain ta nemi karbo aron dan wasan Porto da Portugal Danilo Pereira, mai shekara 29. (Goal)

Dan wasan Kamaru Eric Maxim Choupo-Moting, mai shekara 31, zai sanya hannu kan kwangilar shekara biyu aBayern Munich, bayan barin Paris St-Germain. (Kicker via Goal)