Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
UEFA Ranking: Ƙungiyoyin La Liga sun sha gaban na Premier League
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Manyan ƙungiyoyin Spain guda uku suka mamaye saman teburin ajin matsayi na Uefa na ƙungiyoyin Turai a kakar da aka kammala ta 2019/2020.
Amma Bayern Munich da ta lashe kofin gasar zakarun Turai ta Champions League ita ce ta farko a teburin, yayin da kuma ƙungiyoyin Spain guda uku ke bi mata.
Real Madrid mai riƙe da kofin La Liga ita ce ta biyu, Barcelona da ba ta lashe kofi ba a kakar da aka kammala a matsayi na uku sai kuma Atletico Madrid a matsayi na huɗu.
Juventus ta Italiya ce matsayi na biyar, sai Manchester City daga Ingila a matsayi na shida.
Sevilla mai riƙe da kofin gasar Europa ita ce ta takwas, kafin Manchester United da ke matsayi na tara. Liverpool da ta lashe Premier ita ce ta 10, Arsenal kuma matsayi na 11.
Hakan ya nuna ƙungiyoyin Spain sun sha gaban na Ingila teburin matsayin na hukumar Uefa.
Duk da Tottenham ce ta shida a teburin Premier a kakar da aka kammala amma ta sha gaban Chelsea a ajin matsayin na Uefa wacce ta ƙare a matsayi na huɗu a teburin Premier.
Tottenham ce ta 14 yayin da Chelsea ke matsayi na 16 a ajin matsayin na Uefa.
Ga ajin matsayin ƙungiyoyin Turai daga 1 zuwa 10
Karon farko kenan da Bayern Munich ta sha gaban Real Madrid da ta mamaye matsayi na ɗaya tun kakar 2012/13 da Barcelona ta ɗare teburin, Bayern Munich kuma na bi mata a matsayi na biyu.
Rabon da wata ƙungiya daga Ingila ta kere sauran ƙungiyoyin Turai a matsayin wadda ta fi shahara a Turai tun kakar 2010/11 da Manchester United ta ɗare teburin na Uefa.
A kakar 2011/12 Manchester United ce ta biyu bayan Barcelona sai kuma Chelsea a matsayi na uku a teburin ƙungiyoyin da suka fi shahara a Uefa.
Chelsea ta taɓa zama ta ɗaya a kakar 2007/08, kakar da Chelsea ta buga wasan ƙarshe da Manchester United a gasar zakarun Turai ta Champions League. Manchester United ce ta lashe kofin a bugun fanariti.
Spain ce ta farko a Turai
Spain ce ta ɗaya a jerin matsayin ƙasashen Turai da suka fi shahara a fagen tamola a kakar 2019/20.
Ingila ce ta biyu a teburin, Jamus a matsayi na uku, sai Italiya matsayi na huɗu. Faransa na matsayi na biyar, Portugal matsayi na shida.
Yadda Uefa ke tantance matsayi
Uefa na tantance matsayin daga dukkanin sakamakon wasannin ƙungiyoyin Turai a gasar zakarun Turai ta Champions League da kuma Europa League.
Ana tantance matsayin tawagar ƙasashe bisa sakamakon wasannin da suka buga da kuma damar da ƙungiya ta samu na buga wasanni a kaka mai zuwa.
Sannan Uefa na tantance matsayin ƙungiya ne bisa rawar gani da ta yi a kakar wasanni biyar.