Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Suarez, Alcantara, Bale, Origi, Sancho, Torreira, Koulibaly

ShugabanBarcelonaJosep Maria Bartomeu zai gaya wa dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, cewa za a rage albashinsa. (Deportes Cuatro - in Spanish)

Liverpool za ta jira zuwa makon karshe kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo kafin ta bayyana cewa tana son dauko dan wasan Bayern Munich dan kasar Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (Talksport)

Manchester United ta shirya bai wa dan wasan Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 31, kwangilar takaitaccen lokaci, inda da farko zai yi zaman aro na kakar wasa daya, bayan ta hakura da yunkurin dauko dan wasan Borussia Dortmunddan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Sun)

Sai dai Bale ba ya son zaman aro a a United. (Mail)

Dan wasanBarcelona Luis Suarez yana fuskantar hatsarin kwashe kakar wasa a kan benchi a yayin da ake takaddama a kan kwangilarsa. An gaya wa dan wasan na Uruguay mai shekara 33 cewa zai iya tafiya wata kungiyar amma har yanzu akwai ragowar shekara daya a cikin kwangilarsa. (ESPN)

Manchester United tana fargabar cewa za ta fuskanci kalubale wajen wasu kungiyoyi a yunkurin dauko Sancho idan lamarin ya kai kakar wasa mai zuwa Sancho idan suka gaza dauko shi daga Borussia Dortmund a wannan lokacin na musayar 'yan kwallo. (ESPN)

Manchester City ta mika £82m da kuma karin £4.5m na tsarabe-tsarabe kan dan wasan Atletico Madrid dan kasar Uruguay Jose Gimenez, mai shekara 25. (AS - in Spanish)

Idan Manchester City ko Paris St-Germain ba su kammala daukar dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly ba zuwa karshen mako, ana sa ran Napoli za ta janye dan wasan mai shekara 29 daga kasuwa. (Football Italia)

Manchester United na tattaunawa da Real Madrid kan dan wasan Sufaniya mai sekara 23 Sergio Reguilon. (Marca)