Lionel Messi ya halarci atisaye a filin wasan Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya koma atisaye a filin wasan Barcelona bayan da ya fasa shirinsa na barin kungiyar.
Messi, mai shekara 33, ya mika wa Barcelona takardar saki ranar 25 ga watan Agusta sai dai ranar Juma'ar da ta wuce ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a Barcelona, sakamakon ba zai yiwu wata ƙungiya ta iya biyan farashin da kungiyarsa take nema a kansa ba.
Wannan ne karon farko da dan kasar ta Argentina ya yi atisaye tare da abokansa da ke kungiyar tun bayan zuwan sabon koci Ronald Koeman.
Barcelona za ta yi wasanta na farko a La Liga ta bana ranar 27 ga watan Satumba inda za ta fafata da Villarreal.
Messi bai halarci gwajin cutyar korona da kungiyar ta yi wa 'yan wasanta ranar 30 ga watan Agusta ba kuma bai yi atisaye ba tun bayan da ya aike wa kungiyar takardar son barinta.
Barcelona da La Liga sun dage cewa ba zai bar kungiyar ba sai an biya euro 700m euros (£624m).
Da yake kaddamar da gasar La Liga ta kakar 2020-21 ranar Litinin, shugaban La Liga Javier Tebas ya ce bai "taba damuwa sosai" a kan aniyar Messi ta barin Barcelona a bazara.







