Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Real Madrid da suka doke Real Mallorca
Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Mallorca a wasan mako na 31 a La Liga da za su fafata ranar Laraba a filin wasa na Alfredo Di Stéfano.
Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fuskanci karawar.
A wasan farko da suka fafata ranar 19 ga watan Oktoban 2019, Mallorca ce ta ci 1-0, kuma Lago Junior ne ya ci mata kwallon.
Real Madrid wadda za ta buga wasa na 31 tana ta biyu a teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona.
Barcelona wadda ta buga wasa 31 ranar Talata ta yi nasarar cin Athletic Bilbao 1-0 a Camp Nou ba 'yan kallo.
Real Mallorca tana ta 18 a kasan teburin La Liga da maki 26, saboda haka tana bukatar makin nan domin ta dan yi saman teburi.
Ita kuwa Real Madrid na fatan komawa mataki na daya da zarar ta doke Mallaorca idan anjima.
'Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Real Mallorca:
Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Mendy da kuma Javi Hernández.
Masu buga tsakiyas: Kroos da Modric da Valverde da James da kuma Isco.
Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.