Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sergio Aguero: Raunin da dan wasan ya yi a gwiwarsa ba shi da kyawun gani - Guardiola
Raunin da Sergio Aguero ya yi a karawar da Manchester City ta doke Burnley da ci 5-0 ranar Litinin "ba shi da kyawun gani", a cewar kocin kungiyar Pep Guardiola.
An tilasta wa dan wasan fita ana dab da tafiya hutun rabin lokaci bayan Ben Mee ya doke shi abin da ya kai ga bai wa City bugun fenareti wanda ya sa ta ci kwallonta ta biyu.
Guardiola ya bayyana cewa dan Argentina ya kwashe kusan wata daya yana fama da ciwon gwiwa.
"Za mu duba shi da kyau gobe don mu ga ainihin abin da ke damunsa," in ji kocin na City.
"Ya ji wata alama a gwiwarsa. Tun watan jiya yake jin zafi a gwiwarsa, don haka za mu sake duba shi sosai."
Da aka tambaye shi ko ya damu da yiwuwar hana dan wasan mai shekara 32 karasa kakar wasan bana, sai Guardiola ya ce: "Ni ba likita ba ne, amma dai raunin ba shi da kyawun gani."
Gabriel Jesus ya maye gurbin Aguero a wasan na Litinin wanda City ta lashe cikin sauki, inda Phil Foden da Riyad Mahrez suka zura kwalo bi-biyu sannan David Silva ya ci kwallo ta biyar.
City ta yi nasara a kan dukkan wasannin da ta buga tun da aka koma gasar Firimiya a makon jiya, inda ranar Laraba ta doke Arsenal da ci 3-0.